News
Hukumar NRC ta sanar da jama’a cewa ba ta bullo da tikitin yanar gizo ba a kan titin jirgin kasa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, ta sanar da jama’a cewa ba ta bullo da tikitin yanar gizo ba a kan titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan ba, yayin da ta bukaci fasinjoji da su gaji fadawa hannun masu damfara.
Hukumar ta NRC ta bayyana cewa wasu masu aikata laifuka ta yanar gizo ne suka kirkiri shafin, inda ta bukaci jama’a da kada su ziyarci shafin yanar gizon na bogi domin samun tikitin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan.
Ministocin Tinubu: Majalisa ta tilasta wa Bosun Tijani neman afuwar sanatoci da ‘yan Najeriya
Kakakin hukumar ta NRC, Mista Mahmoud Yakubu, a cikin wata sanarwa ya ce, “NRC ba ta fara sayar da tikitin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan ba.”
A cewar NRC, mai yiwuwa ’yan damfara ne suka yi hakan da nufin zamba cikin fasinjojin jirgin da ba su ji ba basu gani ba.
Hukumar ta NRC ta shawarci fasinjojin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan “su yi hattara da wadannan ’yan damfara ta hanyar samun tikitin shiga jirgin kasa a tashoshin jirgin kasa yayin da NRC ke aiki tukuru wajen bullo da amintattun tikitin kan layi a Legas zuwa Ibadan da Warri zuwa Itakpe na jirgin kasa nan ba da jimawa ba. .
