Connect with us

News

Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Borno

Published

on

Yan bindiga
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Wasu mahara da ake zargi mayaka masu ikirarin jihadi ne sun kashe mutane 13 ciki har da sojoji 3 a jihar Borno  kamar yadda mayakan sa kai da ke aiki da sojojin Najeriya suka bayyana a Lahadin nan.

Advertisement

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kai wannan harin ne a cikin talaitainin daren Asabar zuwa wayewar garin Lahadi a kan wani sansani da ke Wulari, wani kauye da ke kusa da garin Konduga na jihar Borno.

Bauchi na da mafi yawan wadanda ake zargin sun kamu da cutar mashako– BASPHCDA

Daya daga ciki jagororin ‘yan sa kai, Ibrahim Liman ya ce ‘yan ta’addan sun yi amfani da duhun dare da kuma na masara da ke gonakin da ake daf da yin girbi ne wajen kai wa sansanin farmaki.

Liman ya ce dakarun Najeriya sun tinkare ‘yan ta’addan, inda aka yi mummunan ba-ta-kashi, lamarin da ya yi sandin mutuwar sojoji 3.
Wasu majiyoyi sun ce ko a yammacin Asabar, sai da ‘yan ta’adda suka yi wa wasu manoma kawanya a yayin da suke aiki a wata gona, inda suka kashe mutane 10 da ke aiki a cikin gonar.
Kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun tsananta hare-hare a kan masu saran itace, manoma, masunta da ‘yan gwangwan, suna mai zarginsu da yi musu leken asiri.
Akalla mutane dubu 40 ne suka mutu sakamakon rikicin ‘yan ta’adda da aka shafe shekaru 14 ana yi a Najeriya, rikicin da ya bazu zuwa makwaftanta Nijar, Kamaru da Chadi.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *