News
Muna Asarar Sama Da Naira Billiyan 13 A Duk Mako Saboda Rufe Iyakokin Najeriya Da Nijar -AED
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kungiyar zauren cigaban tattalin arzikin Arewa ta bayyana cewa matsakaicin asarar kudi na mako-mako sakamakon rufe iyakokin Nijar da Najeriya ya kai Naira biliyan 13.
Kungiyar ta shaidawa manema labarai a Abuja cewa, ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya na da kwantenar kayan gwari kimnain.dubu 2 da suka makale sakamakon rufe iyakokin wanda ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar ICPC Na Binciken Wasu Jami’ai 5 A Ma’aikatar Gona Da Raya Karkara Ta Kasa
Shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Shehu Dandakata, ya ce bisa kididdigar shekarar 2022, cinikayyar yau da kullum tsakanin kasashen biyu ta kai Naira biliyan 171, yayin da ake kiyasin ciniki na yau da kullum ya kai Nwira billiyan dari 5 da 15, galibi na kayayyaki masu lalacewa.
Ya kara da cewa al’ummar Nijar kusan miliyan 25 ne kuma kusan kashi 70 mazauna garuruwan da ke kusa da Najeriya ne.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
