News
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani Ya Zaftare Kuɗin Makarantun Gaba Da Sakandare a Kaduna

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, a wata sanarwa da ya fitar na rage kuɗaɗen da ake biya a makarantun gaba da Sakandare na jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a yau
Uba Sani ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan koken da al’ummar jihar suka shigar dangane da tsadar kuɗin karatu na manyan makarantun jihar.
Ya ce wannan wani ƙoƙari ne na gwamnatinsa na ganin ta sauƙaƙawa ‘ya’yan ma su karamin ƙarfi, wajen biyan kuɗaɗen karatu a wannan yanayi na matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Uba Sani ya kuma ƙara jaddada aniyar gwamnatinsa, na ganin ta samar da ilimi kyauta a matakan Firamare da Sakandare ga ɗaukacin ɗaliban jihar Kaduna.
Makarantun da Uba Sani ya sanar da rage kuɗaɗen na su akwai Jami’ar jihar Kaduna (KASU) da Kwalejin aikin lafiya na Shehu Idris da ke Makarfi da kuma Makarantar koyon aikin jinya ta jihar Kaduna da aka rage yawan kuɗaɗensu da kaso 30 cikin ɗari.
Haka nan kuma Gwamna Uba Sani ya sanar da rage kashi 50 cikin ɗari na kuɗaɗen a makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic da kuma kwalejin ilimi na Gidan Waya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwar da cire tallafin man fetur ya jefa ƙasar a ciki.