News
Tambayoyi 101 Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano – Daga Bello Galadi
Daga Bello Galadi.
A ranar Laraba, 20 ga Satumba, 2023, Alkalai uku na Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna kano suka zartar da hukunci bisa dalilai guda uku (3) wanda suka dadadawa masu kara na kara . Dalilan kuwa sune: (1) Cewa Abba Kabir Yusuf bai cancanci tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a ranar 18 ga Maris, 2023 ba saboda shi ba dan jam’iyyar NNPP ba ne . (2) Cewa akwai gagarumin rashin bin dokar zabe dangane da aringizon kuri’u , soke zabukan wasu mazabu saboda rikici, lalata kayayyakin zabe, barazana ga rayukan jami’an zabe da kuma hana su hakkokinsu. (3) Cewa Abba bai samu mafi rinjayen halasttun kuri’un da aka kada a zaben ba.
NSCDC Sun Cafke Matashin Da Ya Sace Babur Din Abokin Mahaifinsa A Jigawa
Manyan yan takarar gwamnan Kano biyu sune, Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna {wanda ake kira “Gawuna”} sai kuma na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf (wanda ake kira “Abba”).
A karshen zaben, INEC ta bayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 1, 019, 602, inda ya doke Gawuna wanda ya samu kuri’u 890, 705. Tazarar kuri’u 128,897 a tsakanin su kamar yadda INEC ta sanar.
Kotun ta warware batu na 1 wanda ya farantawa masu shigar da kara. Watau kotun ta amince da bukatar masu shigar da kara cewa Abba ba dan jam’iyyar NNPP ba ne saboda babu sunansa a rajistar zama mamba na jam’iyyar NNPP kamar yadda aka yi ranar zabe.
Tare da girmamawa ga alkalan, na kasa aminta da hujjojin su. A siyasa, bayyanawa jama’a cewa kai dan jam’iyyar siyasa ne kawai ya isa mutum ya cancanci zama dan jam’iyyar siyasa ko da babu sunan sa a cikin rajistar zama memba.
Kotun ta kuma amince da bukatar masu shigar da kara cewa akwai gagarumin rashin bin dokar zabe yayin zaben. Watau kotun ta amince da masu shigar da kara cewa an samu aukuwar lamarin da ya hada da aringizon kuri’u , soke zaben saboda tashe-tashen hankula, lalata kayayyakin zabe, kawo cikas da gangan, barazana ga rayuwar jami’an zabe, ba su hakkokinsu da sauran kura-kurai, dalilin da ya sa kotun ta soke akalla kuri’u 231, 843.
Yadda aka saba, a duk lokacin da mai shigar da kara ya samu nasarar gabatar da gamsashiyar hujja ta rashin bin dokar zabe, umarnin da ya dace da Kotun ta yi sabon zabe ne, ba bayyana wanda ya yi nasara ba. Me yasa wannan shari’ar ta bambanta?
Haka dai kotun ta amince da bukatar masu shigar da kara cewa Abba bai samu mafi rinjayen halasttun kuri’un da aka kada ba. Kotun ta amince cewa Gawuna ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada. Kotun ta bayyana cewa kuri’u 165, 663 da aka zabi Abba da su a karamar hukumar Tarauni ba halasttun ba ne, saboda rashin tantancewa – babu tambari, babu sa hannu, babu kwanan wata. Kotun ta cire kuri’u 165, 663 daga kuri’u 1, 019, 602 na Abba sannan ta ce halasttun kuri’un da aka zabi Abba da su sune 853, 939 .
Ni dai ban yarda da matakin da alkalai suka dauka ba na soke halasttun kuri’u. Sashe na 63 (2) na Dokar Zabe, 2022 ya wa: “Idan Jami’in zabe dya gamsu da kuri’u ko da babu sitamfi ko sa hannun sa, indai ya yarda daga cikin littafin kuri’un hukumar zabe aka yanko shi, kuma har aka kada ta a matsayin an yi zabe to shi ko ita, duk da rashin alamar hukuma, zai kirga waccan kuri’ar zaben”.
Ina Wakilan Jam’iyyar APC a lokacin da ake tantance kuri’ar zaben? Ta yaya suka bari aka kirga ta a cikin kuri’un zabe da ba a tantance ba tun farko? Ina jami’an hukumar zabe ta INEC lokacin da ake zargin an shigo da takardun zaben da ba a tantance ba a cikin akwatunan?
Mu dauka ace Kotun ta yi gaskiya cewa ainahin kuri’un da Abba ya samu sune 853,939, sannan Gawuna ya sami 890,705, to jimillar kuri’u da aka soke sun kai 231, 843 Kuma haka ya nuna kuri’u da aka soke sun fi wadanda aka bada tazarar dasu na 36, 766 a tsakanin yan takarar biyu .
A wannan yanayi, ni a ra’ayi na kamata yayi zaben ya zama cewa bai kammala ba, kamata yayi a sake zabe, Me ya sa Kotun ta ayyana Gawuna a maimakon bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe da abin ya shafa?
Sashe na 24 (4) & (5) na Dokar Zabe, 2022 . Ba za’a bayyana wanda ya ci zabe ba, har sai an sake yin zabe a yankunan da abin ya shafa. Za a iya bayyana sakamakon zaben ne kawai idan an gamsu cewa sakamakon zaben ba zai shafi zabe a yankunan da abin ya shafa ba.
A WANNAN AL’AMARI, SAKAMAKON ZABEN YA SHAFI YANKUNAN DA ABUN YA SHAFA.
Wani babban al’amari da ya ja hankalina shi ne yadda kotun ta bayar da umarnin da ya shafi Gawuna wanda baya cikin masu kara. Da farko dai ya zabi rungumar kaddara, Inda har ya taya Abba murna. Don haka bai cancanci cin gajiyar sakamakon Shari’ar ba. Hakan ya sabawa, hukuncin Kotun Koli ta yanke cewa: “Hukunci tare da oda, a kan hana mutumin da ba ya cikin wata kara Kuma ya ci moriyar wannan karar shi da wani amfani”.
Wani al’amari mai ban mamaki shi ne yadda INEC da NNPP ba su gabatar da shaida ko daya, kuma a matsayinsu na wadanda ake kara, sai dai sun dora a shari’arsu ne kan shari’ar wadanda suka shigar da kara.
Hakan taimaka wajen nakasa Shari’ar da sukai su da kansu. Me ya sa lauyoyin INEC da NNPP biyu (2) basu gabatar da hujjoji ba? Batun koke-koken zabe suna da tsauri, don haka, suna bukatar ayi taka-tsan-tsan da su. Wasu lauyoyin da suka ɗauki irin wannan tsari a baya har yanzu suna nadamar ayyukansu.
Abba ya kira shaida guda daya, Baffa Bichi. Me zai sa Abba zai dogara da shaida guda daya a irin wannan lamarin mai girma wanda shi ne zai fi kowa amfana da an yi nasara?
Na yi imani, Kotunan daukaka kara za su gyara kurakuran da aka yi, za su sanya dokokin a mahallan da suka dace, sannan su fito da ingantattun maganganu masu inganci wadanda za su tafi da hukuncin da akai a baya.
Galadi tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Gusau (mai kula da jihar Zamfara). Shine Shugaban Gidauniyar Bello Galadi.
Ana iya samun shi akan:
Muhammadbel_law@yahoo.com and muhammadbella
w80@gmail.com and twitter handle:@bello_galadi1