News
An Tsinci Jariri A Gona A Jahar Jigawa
SAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An gano wani jariri da aka yar da shi a gona a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa da safiyar Lahadi.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Wani manomin da ke aiki a gonarsa ne ya tsinci yaron a cikin gona , inda nan take ya sanar da Hakimin kauyen Wurya da ke Gwaram Tsohuwa faruwar lamarin.
Tambayoyi 101 Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano – Daga Bello Galadi
Alhaji Tamaji Gwaram, mataimakin shugaban karamar hukumar Gwaram, ya ce sun fara kai jaririn zuwa ga jami’in ‘yan sanda na karamar hukumar Gwaram, daga bisani kuma suka kai shi asibiti, inda aka tabbatar da lafiyarsa.
A cewarsa, an mayar da jaririn ga shugaban karamar hukumar, Zaharaddeen Abubakar, inda nan take ya bukaci a nemo wata mata da za ta iya kula da shi.
Rukayya Aliyu, wadda ta sadaukar da kanta wajen kula da jaririn,tace ta yi hakan ne da izinin mijinta, Hakimin Wurya, Malam Aminu Abdul-Hamid.
Daga baya aka sanya wa jaririn suna Zaharadden, sunan shugaban karamar hukumar, kamar yadda kuma sabon gidan suka sa masa suna Aminu, mai cikakken sunansa da Zaharaddeen Aminu Gwaram.
Alhaji Tamaji Gwaram ya ci gaba da bayyana cewa shugaban karamar hukumar ya kuma yi alkawarin ba magidanta alawus-alawus duk wata baya ga sauran tallafin da ya kamata, akalla har zuwa karshen wa’adinsa na shugaban karamar hukumar Gwaram.
Wani labarin kuma Tambayoyi 101 Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano – Daga Bello Galadi
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro