Connect with us

News

Taɓarɓarewar Tsaro: Majalisar Dattawa ta gayyaci Nuhu Ribadu da shugabannin tsaro

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Majalisar Dattawan Nijeriya ta ƙuduri aniyar yi wa hafsoshin tsaron ƙasar kiranye, saboda taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman Arewacin Nijeriya.

Majalisar Dattijai ta ɗauki matakin ne a jiya Alhamis bayan tattaunawa kan batutuwan yin garkuwa da wasu ɗalibai mata guda biyar na Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma dake Jihar Katsina a ranar Laraba bayan da Sanata Yar’Adua mai wakiltar yankin Katsina ta Tsakiya a majalisar ya gabatar da ƙudirin.

Advertisement

Maulidi: an samarwa da al’ummar kasa da duniya baki daya hanyar yayewar masuf -shekh abdulwahid  al’karmawi

Waɗanda za a gayyace sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Shugaban Hafsan Sojin Sama, Air Marshall Hassan Abubakar.

Sauran waɗanda za a gayyata sun haɗa da; Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olukayode Egbetokun da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu

Advertisement

’Yan majalisar sun buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da ɗaliban mata da aka sace da kuma sauran waɗanda da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Sun bukaci sojoji su gudanar da ayyuka na musamman domin fatattakar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan.

Advertisement

 

 

Advertisement

Sanatocin sun kuma jaddada buƙatar samar da ‘yan sandan jihohi a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.

Har yanzu ba a ƙayyade ranar da aka shirya yin ganawar da hafsoshin tsaron ba.

Advertisement

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne suka yi awon gaba da ɗaliban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke jihar Katsina, aqalla biyar, inda ’yan sanda suka tabbatar da kama ɗaya da ake zargi da hannu a lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending