News
Hukuncin kotu koma baya ne na ɗan karamin lokaci – Dauda Lawal
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka kara a matsayin koma baya na wucin gadi.
A ranar Alhamis ne kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar ta Zamfara a matsayin wanda bai kammala ba.
Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da zaɓ a kananan hukumomi uku da suka haɗa da Maradun, Birnin-Magaji da Bukkuyum.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Juma’a, gwamna Lawal ya ce an zaɓe shi ne saboda ya tsame jihar daga halin kunci da take ciki.
A cewarsa, sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, ya nuna abin da mutane suka zaɓa musamma na ganin an samu canji mai kyau da kuma ci gaba.
Ya ce: “Hukuncin da kotun ɗaukaka kara ta yanke, koma baya ne na ɗan lokaci. Duk da haka, ina da kwarin gwiwar cewa abin da mutane suka zaɓa shi za a basu.
Ya yi kira ga al’ummar Zamfara da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce tawagar lauyoyinsa na nazari sosai kan hukuncin domin ɗaukar matakin da yaq dace.
A wani labarin kuma Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Shugabannin APC/NNPP sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Kano
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
