Connect with us

News

Kotu ta yan kewa mai yin lalata da almajirai ta dubura hukuncin ɗaurin rai da rai

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Babban kotu a Birnin Kudu a ranar Alhamis ta yanke wa Israfilu Sagiru mai shekara 25 mazaunin kauyen Zarena dake karamar hukumar Birnin Kudu hukuncin daurin rai da rai bisa laifin yin lalata da yara maza biyu.

An fara gurfanar da Sagiru a gaban kotun ranar 5 ga Satumbar 2021 bisa laifin yi wa almajirai maza masu shekaru 11 da 12 fyade.

Advertisement

Tsawa Ta Kashe Masu Garkuwa Da Mutane Su 3 A  Jihar Kwara

An gano cewa Sagiru kan lallabi wadannan yara da sunan zai basu sabbin kayan sawa idan suka zo wurinsa. Bayan sun yarda sun zo ne yake yin lalata da su.

Fannin da suka shigar da karar sun gabatar da shaidu uku, takardan bayanin laifin da Sagiru ya rubuta da sakamakon gwajin da aka yi a asibiti akan wadannan yaran.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa A dalilin haka ne alkalin kotun Musa Ubale ya yanke wa Sagiru hukuncin daurin rai da rai.

A wani labarin kuma Tsawa Ta Kashe Masu Garkuwa Da Mutane Su 3 A  Jihar Kwara

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending