News
Kaso 7 cikin 10 Na Daliban Najeriya Na Aikata Laifukan Zamba Ta Yanar Gizo – Shugaban EFCC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede, ya bayyana damuwarsa kan yadda matasan Najeriya ke tafka ta’asa wajen aikata laifuka ta yanar gizo.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X(twitter), Olukoyede ya ce abin damuwa ne yadda dalibai a Najeriya kusan kimanin kaso 7 cikin 10 a Najeriya ke tafka laifuka na yanar gizo.
Shari’ar Zaben Gwamnan Kano: Yau Kotun Koli Za Ta Saurari Shari’ar Abba Da Gawuna
Rahotanni na nuni da cewa Shugaban na EFCC ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tawagar Daar Communication PLC da suka kai ziyarar ban girma a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja.
“Muna bukatar hadin kan kamfanin sadarwa irin Daar wajen fadakar da matasanmu kan illolin da ke tattare da aikata laifuka ta yanar gizo, abin damuwa ne a ce kashi 7 cikin 10 na illahirin daliban Najeriya a yau suna aikata laifukan yanar gizo,” in ji Olukoyede.
Shugaban na EFCC ya yi kira ga kafafen yada labarai da su tsara shirye-shirye da nufin fadakar da matasan Najeriya game da illolin muggan laifuka musamman wadanda suka shafi yanar gizo.
Shugaban na EFCC ya ci gaba da cewa “wadannan su ne matasan da mu ke sa ran za su zama shugabannin gobe, ya kamata kafafen yada labarai su jajirce wajen wayar musu da kai kan munanan ayyuka da illolin ta’addanci.”
A wani labarin kumaShari’ar Zaben Gwamnan Kano: Yau Kotun Koli Za Ta Saurari Shari’ar Abba Da Gawuna
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
