News
An Gurfanar Da Wasu Ma’aurata A Kotu Kan Zargin Sace Budurwa Jihar Kano.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An gurfanar da wasu ma’aurata kan zargin sace budurwa a Karamar Hukumar Tudun Wada da ke Jihar Kano.
Mata da mijin sun gurfana a gaban Kotun Majistare da ke zama a unguwar Nomansland da ke Kano ne bisa zargin hada baki da kuma sace budurwar mai shekaru 17.
Yan Sanda Sun Kama Wani Mai Kwacen Waya Da Ya Guntule Yatsun Matashi
Rahotanni na nuni da cewar sun musanta zargin sace budurwar bayan dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Fago Lale, ya karanta musu tuhumar a gaban alkali.
Lauyansu ya nemi belinsu, yana mai cewa sun shigar da kara a babba kotun jihar suna neman a hana Kwamishinan ’yan sanda da kuma DPO na Tudun Wada tauye musu hakkinsu na dan Adam.
Amma alkalin kotun majistaren, Ibrahim Mansur Yola, ya bayyana cewa kararrakin ba su da alaka, saboda wancan na hakkin dan Adam ne, wanda ke gabansa kuma na zargin aikata laifi ne.
Sannan ya ce tsare wadana ake zargin a hannun hukuma ya fi zamansu a gidansu, saboda haka ya ba da umarnin tsare su.
Daga nan ya dage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Janairun da muke ciki.
A wani labarin kuma An Gurfanar Da Wasu Ma’aurata A Kotu Kan Zargin Sace Budurwa Jihar Kano.
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
