Connect with us

News

Ba mu yarda da maida ofisoshin CBN da FAAN, Legas ba – Sanatocin Arewa

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Kungiyar Sanatocin Arewa NSF ta yi Allah-wadai da mayar da wasu sassan babban bankin Najeriya da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa FAAN daga Abuja zuwa jihar Legas.

Advertisement

Sanatocin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta canja shawara tun da wuri ko kuma su haɗu a kotu.

Gwamnatin Tarayya Ta shirya Kaddamar Da Shirin Baiwa Dalibai Bashi 

Suleiman Kawu, mai magana da yawun NSF ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Advertisement

Babban bankin na CBN a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata ya bayyana shirin mayar da wasu sassan nasa zuwa Legas saboda kasancewar hedikwatarsa da ke Abuja na cike da cunkoso na ma’aikata.

Hakazalika, ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo shi ma ya sanar da mayar da hedikwatar FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Advertisement

Mista Kawu, dan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana cewa ‘yan Arewa ba su gamsu da mayar da hukumomin gwamnatin tarayya biyu zuwa Legas ba.

Ya ce Sanatocin Arewa sun fara tattaunawa da takwarorinsu na sauran shiyyoyin domin ganin an mayar da sassan da aka mayar da su a hukumomin tarayya biyu zuwa Abuja.

Advertisement

Baya ga sanatocin kungiyar dattawan Arewa sun nuna ɓacin ran su a baya cewa yin haka hanya ce kawai na gurgunta yankin Arewa.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending