Politics
Ina Roƙon Abba Gida-Gida Ya Dawo APC — Ganduje
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya roƙi gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Ganduje, wanda shi ne tsohon gwamnan Kano da Abba Kabir ya gada, ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na APC da aka yi a Kano a yau Alhamis.
Wannan kira na Ganduje na zuwa ne kusan mako guda bayan da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi shawarar cewa ya sasanta da jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bayan da Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kanon.
A ƙarshen taron, Ganduje wanda ya gana da manema labarai ya sha alwashin jawo hankalin dukkan ƙananan jam’iyyu su koma ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Ya kuma tabbatar da cewa APC za ta bai wa Abba Gida-Gida da magoya bayansa duk wata dama ta jin daɗin zama a jam’iyyar.
“A yanzu mun yi nasarar jawo hankalin wasu gwamnoni don su shiga APC. Nan ba da daɗewa ba wasu gwamnoni za su shigo jam’iyyarmu. To idan har za mu iya yin hakan a matakin ƙasa, me zai hana mu iya yi a matakin jiha?
“Hannayenmu a buɗe suke. Muna roƙon duk waɗanda ke son shigowa jam’iyyarmu. Musamman, muna gayyatar gwamnan Kano da ya bar jam’iyyarsa ta NNPP ya koma APC.
“Muna kira gare shi. Mun yi alkawarin samar da yanayi mai kyau ga gwamnan da Jihar Kano ta yadda za mu samar da mabiya masu yawa.
“Wannan shi ne kwatankwacin yawan al’ummarmu tun da mu ne jiha mafi yawan jama’a a tarayya,” a cewar shugaban na jam’iyyar APC.
Shi ma a nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce sun yi taron ne a kokarin yi wa umarnin Shugaba Tinubu biyayya, wanda ya nemi su bude kofofin jam’iyyar ga masu son shigowa cikinta.
Rahotanni na nuni da cewa wasu daga cikin kusoshin jam’iyyar APC da suka halarci taron sun hada da Karamin Ministan Gidaje, Abdullahi T Gwarzo, tsohon Sanatan Kano na Arewa, Kabiru Gaya, tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji da dan takarar mataimakin gwamnan Kano na APC a zaben 2023, Murtala Sule Garo.
Haka kuma, duk tsofaffin kwamishinoni da shugabannin hukumomi da ma’aikatun Kano na gwamnatin Ganduje sun halarci taron.