Connect with us

News

Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum hudu suka yi garkuwa da wasu a Zurmi

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

A wani hari da suka kai lokuta daban-daban a kauyukan dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara ƴan bindiga sun kashe mutum hudu sannan sun yi garkuwa da mutane da dama daga yankin.

Maharan sun saci dabbobi sannan sun ƙona gida wani mutum ɗaya a ƙauyen.

Wani Matashi Ya Yi Yunkurin Hallaka Kansa Kan Bashin Miliyan Biyu A Jihar Kano

Wani Shugaban matasa a Zurmi Abubakar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa harin farko ya auku ne ranar Talata a Yanbuki sannan na biyu a Baichen Dauran ranar Laraba.

“A harin farko maharan sun yi wa wasu matafiya fashi bayan sun tsayar da motar su a Dutsi Uku sai dai kafin su yi wani barna ‘yan banga sun iso wurin inda suka fatattake su.

Abubakar ya ce daga nan sai maharan sanye da rigunan sojoji suka kara kai wa kauyen Baichen Dauran hari da karfe 12 na dare.

Advertisement

Ya ce ko da suka shigo kauyen maharan sun fara kwashe dabbobin mutane ne amma da mutane suka fara gudu sai suka fara harbin su.

“Da gari ya waye ne mutane su ga cewa maharan sun kashe mutum biyu wasu mutum hudu sun ji rauni.

“Maharan sun kuma tafi da mutane da dama daga kauyen inda da dama daga cikin su mata da yara kananan ne.

Majiya daga kauyen Ahmad Dauran ya ce daya daga cikin mutanen da maharan suka kashe abokinsa ne Abubakar Danjuma.

Dauran ya kuma ce ‘yan bindigan sun Kona gidan wani dan kasuwa Lawal Mati inda a cikin gida akwai kayan abinci da babura.

Ya ce a makon jiya maharan sun kashe mutane uku Kuma sun yi garkuwa da mutane da dama a kauyen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending