News
Tsadar Rayuwa: Kasuwancin Awara Ya Bunƙasa A Sanadiyyar Ɓarkewar Yunwa A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Awara, wani nau’in kayan abinci ne na gida da ake yi daga Waken Soya, yanzu haka ana tsananin bukata ta a yankuna da dama na birnin Kano, sakamakon damuwa da yanayin yunwa da ake ciki a kasar.
Binciken da Wakilinmu ya gudanar ya nuna cewa awara wanda ake soyawa da man gyaɗa ko man kayan lambu kamar ƙosai (Akara) ko Fanke, ta zama abincin yau da kullum a tsakanin jama’ar gari, mai biye mata sai shinkafa da wake, ko tuwo wanda ake yi da garin masara ko dawa ko kuma shinkafa.
Farashin Fetur Ya Kai N700 Duk da NNPC Yayi Alkawarin Kudin Mai ba Zai Tashi ba
Kafin wannan lokaci, amfi amfani da awara a matsayin abin marmari a sassan babban birnin kasuwanci wato Kano.
Binciken da muka yi a wasu wurare daban-dabam waɗanda suka haɗar da kasuwanni da tituna da kuma wasu muhimman wuraren waɗanda aka killace a birnin, an gano cewa mutane musamman matasa sun koma sayen awara saboda tana da arha idan aka kwatanta da shinkafa da wake, ko Tuwo ko shinkafa-dafa-duka (Jallof).
Bincken ya gano cewa da kuɗin ka N200 ko N300 ya isa karin kumallo ko abincin rana ko ma abincin dare, dangane da bukatar mai saye da kuma lokacin da yake buƙatar.
A wasu wuraren sayar da abinci, sakamakon binciken ya nuna cewar awara ana soyata da kwai ko kuma a haɗa ta da yaji kamar su (pappy), ko ganyan salak ko kabeji da kokwamba, wanda hakan ya kan ƙaramata armashi kuma farantin ya ƙara auki domin samun ƙoshi da ƴan kuɗi kalan.
Daya daga cikin masu sayen awara, Kabiru Saleh, ya shaida wa Wakilinmu cewa kusan kullum sai ya sayi awara ya ci a matsayin abincin karin kumallo ko na abincin rana, ” wanda ya danganta da halin da ake ciki na tattalin arziki.”
“Da safe na kan sai awara ta naira 200, a maimakon ƙosai wanda a haɗin yanzu ƙosan ɗari biyu ba a bakin komai yake ba. Amma awara ta wannan kuɗin tana gamsar da ni, da gaske,” inji matashi ɗan shekara 20.
Shi ma wani mai sayen awara mai suna Usman Mahir cewa ya yi ya na sayen awara a matsayin abincin rana a kullum, saboda ya na ganin ta fi shinkafa-da wake arha.
“Da naira 300 na, ina sayen awara don cin abincin rana, kamar yadda na saba maimakon shinkafa- dafadika, wacce ta fi ƙarfina a yanzu. Na sami awara mai rahusa da gamsarwa, “Mahir ya ce.
Wata mai sayar da kayan abincin mai suna Uwani Garba, ta ce tana jin dalin sana’ar sayar da awara ga abokan cinikinta, inda take cinikin kusan naira 20,000 a kowace rana.
“Kafin nan, ina sayar da kosai, amma sai na koma sayar da awara saboda tashin gwauron zabi da farashin wake ya yi wanda a yanzu ake sayar da shi naira 2,500 a kowane mudu.
“Amma waken soya yana da arha, ana sayar da shi a kan N1,300 a kowane kwano. Ina sayen kwana waken soya biyu ko uku wanda daga shi nake yin awara, kuma ina godiya ga Allah ina samun riba mai kyau daga sana’ar”, in ji Garba.
Idan za a tuna Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a makon da ya gabata ya yi shela cewa jihar tana fuskantar barazanar yunwa, yana mai bayyana yanayin a matsayin mai tayar da hankali.
Gwamnan wanda ya sanar da haka a lokacin da yake ganawa da ƴan kasuwa a jihar, ya ce zai nemi Shugaba Bola Tinubu ya sa baki tare da magance matsalar yunwa a jihar Kano.
“Ni da kaina zan je na roki Shugaba Bola Tinubu ya sa baki ya duba yanayin yunwa da ake ciki a jihar Kano, ta yadda za a ceto mutanenmu daga yunwa”, in ji Yusuf.
“Mun san cewa sauran sassan kasar nan na fuskantar irin wannan matsalar, amma za mu yi magana akan jihar Kano, kasancewar ita ce yankinmu kuma ita Allah ya ɗora manan auyin kula da ita”, in ji Gwamna.
