Connect with us

News

Noman Damina Kaɗai Ba Zai Iya Magance Wa Najeriya Matsalar Tsada Da Ƙarancin Abinci Ba – Ƙaramin Ministan Noma

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƙaramin Ministan Noma Aliyu Sabi, ya bayyana cewa Najeriya ba za tsaya kawai ta dogara da noman rani kaɗai ba, muddin ta son tsallake siraɗin matsalar tsada da ƙarancin kayan abinci.

Advertisement

Ministan ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels, a ranar Litinin.

Ta Yiwu Zaɓen Ƙananan Hukumomi Zai Koma Hannun INEC —Majalisar Wakilai 

“Mun fahimci cewa a shekarun baya ba mu ɗaukar noman rani da muhimmanci, to kuma ba za mu iya dogaro da noman damina kaɗai ba wajen samun wadatar abinci,” cewar ministan.

Advertisement

Sabi ya ƙara da cewa gwamnati na bakin ƙoƙarin ta sosai wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta, ta hanyar shirya tsare-tsaren bunƙasa abinci a tsawon kowace shekara, ba sai lokacin ruwan damina kaɗai ba.

“Gwamnati na nan na shirin shigo da motocin noma tarakta guda 2000 a karon farko, daga nan kuma sai a ƙara antayo guda 10,000.

Advertisement

“Duk za a bijiro da waɗannan cikin wani lokaci, yadda za a bunƙasa yawan kayan noma da kuma sauƙaƙe manoma dabaibayin da ke hana su samun ci gaba ta fuskar noma.”

Premium Times ta ruwaito cewa Najeriya ta afka cikin tsadar rayuwa ta yadda a cikin wannan makon Hukumar NBS ta ce malejin tsadar abinci ya dangwale kashi 40.87, yayin da burkin haƙurin ‘yan Najeriya ya tsinke daidai gangara.

Advertisement

Jadawalin tsadar rayuwa da raɗaɗin hauhawar farashin kayan abinci da kayan masarufi wanda Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Litinin ɗin nan, sun nuna cewa malejin tsadar kayan abinci ya dangwale zuwa kashi 40.87% bisa 100% a watan Yuni, 2024.

Hakan na nuni da cewa ya ƙaru da kashi 15.62% bisa 100% idan aka kwatanta da gejin sa na watan Yuni 2023, inda a lokacin yake daidai kashi 25.25% bisa 100%.

Advertisement

Haka kuma NBS ta ce malejin game-garin tsadar rayuwa ya haura zuwa kashi 34.19% bisa 100%.

Ƙididdigar ta NBS, wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, tattabar da cewa tsawon watanni biyar kenan aka shafe duk wata kayan abinci da kayan masarufi na fuskantar tashin farashi.

Advertisement

Najeriya ce dai ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a Afrika, kuma ƙasa mafiya yawan jama’a a Afrika.

Sai dai kuma ‘yan ƙasar sun afka cikin masifar tsadar rayuwa tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, a ranar 29 ga Mayu, 2023 tun a wurin da aka rantsar da shi

Advertisement

Tsadar rayuwa ta ƙara tsamari yayin da gwamnatin Najeriya ta yi sagegeduwar sakacin da darajar Naira ta karye a kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

Duk da masifar tsadar rayuwa da ake fama a ƙasar, har yau ana kiki-kaka wajen kasa samun matsaya dangane da batun ƙarin mafi ƙanƙantar albashi, wanda fiye da shekara ɗaya ake ta tsallen-gada a kan sa.

Advertisement

Wannan sabuwar ƙididdiga ta NBS, ta zo yayin da ‘yan Najeriya ke ta kartar ƙasar furucin shirin fitowa su yi wa gwamnati zanga-zanga a ƙarshen watan Yuli.

Idan aka kwatanta malejin tsadar rayuwa na watan Yuni 2023, za a ga ya tsaya ne daidai kashi 22.79. Yanzu kuwa a Yuni 2024, ya dangwale zuwa kashi 33.95, inda cikin shekara ɗaya aka samu ƙarin gwauron tashi da kashi 11.40.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending