Connect with us

Business

Ba Mu Sanya Farashin Man Fetur Ba – Matatar Man Dangote

Published

on

Matatar Man Dangote ta zargi hukumar NUPRC da gazawa wurin gudanar da ayyukanta
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rukunin Kamfanonin Dangote ya musanta rahoton da ke cewa zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya a kan N600.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar ranar Talata ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi watsi da rahoton da ya ambato ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) tana cewa hamshaƙin attajirin zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya ta fetur a kan N600.

Advertisement

NELFUND Ya Yi Kashedi Akan Shafin Yanar Gizo Na Yaudara Da Ke Ikirarin Bayar Da Tallafin Bizar Kasar Waje

“Muna so mu yi bayyana cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ba ƙawar kasuwancinmu ba ce kawo yanzu. Ba mu taɓa tattaunawa da ita ba a game da farashin man fetur, kuma ba ta da iko ko hurumin yin magana a madadinmu, mai daɗi ko mai tattare da ɓoyayyiyar manufa,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “muna kira ga al’umma su guji watsa jita-jita. Muna da hanyoyin isar da saƙonninmu waɗanda masu ruwa da tsaki suka sani.”

Kamfanin Dangote ya fitar da sanarwar ce a daidai lokacin da ya sha alwashin soma sayar da man fetur a watan nan na Agusta, kamar yadda Anthony Chiejina ya shaida wa wata jaridar Nijeriya.

Advertisement

A baya, kamfanin ya sanar da cewa zai soma sayar da fetur a watan Yuli, sai dai ya jinkirta soma yin hakan saboda wasu dalilai da suka haɗa da tashin gobara a wani ɓangare na kamfanin, kamar yadda attijiri Aliko Dangote ya bayyana.

 

 

Advertisement

TRT Afrika

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *