Connect with us

News

Cutar Mashako Da Kwalara Na Ci Gaba Da haifar da babbar illa ga rayuwar al’umma —Dr Labaran

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da Breakthrough Action Nigeria ta shirya taron karawa juna sani na kwanaki 3 akan Cutar Mashako da Kwalara.

A jawabinsa na bude taron da aka gudanar a Kano kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa, matsalolin kiwon lafiyar jama’a kamar kwalara da Cutar Mashako na ci gaba da haifar da babbar illa ga rayuwar al’umma musamman a lokacin barkewar cutar.

Za Mu Janye Ƙarar Da Mu Shigar A Gaban kotu akan NNPCL  Da Sauransu – Masana’antar Dangote

Ya yi nuni da cewa, don haka ya zama wajibi a yada sakonnin da suka dace, ba wai kawai a sanar da jama’a ba, a’a, don baiwa al’umma damar daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar kwalara da Cutar Mashako, yana mai imani cewa hakan zai magance munanan bayanai da kuma gurbatattun bayanai da ke hana kokarin yakar cututtuka yadda ya kamata.

Dokta Labaran wanda ya samu wakilcin mukaddashin sakataren ma’aikatar Shehu Sani Shehu, ya bukaci mahalarta taron da su bullo da sakonnin da za su wayar da kan jama’a game da illolin Cutar Mashako da kwalara da yadda za su kare kansu da sauran su daga barazanar da ta iya haifarwa.

Wani bangare na makasudin bitar, Shugaban Breakthrough Action Nigeria, Ahmad Muazu, ya bayyana cewa shine samar da daidaito da sahihan sakonnin sadarwa game da cutar kwalara da Mashako, alamomi da magungunan da suka dace da al’ummomi daban-daban a fadin jihar da ma sauran sassan jihar.

Advertisement

 

Dakta Labaran ya bayyana cewa, kungiyoyin za su kasance dandali na inganta harkokin kiwon lafiya, da wayar da kan jama’a kan cututtuka masu yaduwa da wadanda ba masu yaduwa ba tare da samar da al’adun wayar da kan matasa kan kiwon lafiya.

Ya kuma yabawa shirin Breakthrough Action Nigeria bisa yadda suka bada gudumawar bitar tare da jajircewarsu wajen ciyar da lafiyar al’umma gaba a jihar Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending