Connect with us

News

Nijeriya Na Fuskantar Barazanar Durƙushewa – Cewar Peter Obi

Published

on

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Mista Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan halin da ƙasar Najeriya ke ciki, yana mai cewa ƙasar na kan hanyar durƙushewa sakamakon matsalolin da ke ƙaruwa a kowace rana.

Da yake jawabi a taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar LP da aka gudanar a birnin Abuja a ranar Laraba, Obi ya jaddada cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya musamman ‘yan adawa su riƙa magana da gaskiya game da halin da ƙasa ke ciki, domin ceto ta daga tabarbarewar da ke gabanta.

NBC Ta Haramta Saka Waƙar “Tell Your Papa” Ta Eedris Abdulkareem: Sako Mai Cike Da Caccaka Zuwa Ga Seyi Tinubu

“A yau Najeriya na fuskantar barazana sosai. Alƙaluma na nuna cewa yawan talauci na ƙaruwa. Mutane da dama da a baya ke rayuwa cikin walwala yanzu sun fada cikin ƙuncin rayuwa. Wannan na nuna yadda abubuwa ke tabarbarewa,” in ji Obi.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda ko da ziyara yake kaiwa wasu wurare, babu ƙarin girmamawa ko kulawa kamar da. “A da idan na zo, mutane kan tambaye ni abin da nake so na ci ko na sha, amma yanzu babu wanda ke tambayata. Wannan alama ce ta yadda rayuwar mutane ke ƙara shiga mawuyacin hali,” in ji shi.

Obi ya nemi a tashi tsaye, musamman daga cikin jam’iyyarsa ta LP, domin ɗaukar matakan ceto Najeriya daga wannan mummunan hali. Ya ce lokaci ya yi da za a bar bambancin siyasa gefe a yi aiki tare don gyaran al’amuran ƙasa.

Wannan kira na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsaloli daban-daban, ciki har da hauhawar farashin kayayyaki, rashin tsaro da kuma ƙarancin abinci, wanda ke kara jefa miliyoyin ‘yan ƙasa cikin talauci.

Advertisement

 

PRNigeria

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending