Connect with us

News

Ƴan Bindiga Sun Sace Matar Dagaci Da Diyarsa A Kaduna

Published

on

Wasu ƴan bindiga sun sace matar Dagacin Aboro da ke Ƙaramar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, Harira Abdullahi, da kuma diyarsa, Maryam Suleiman Galadima.

lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:36 na dare a ranar Lahadi, lokacin da ƴan bindigar suka shigo gidan Dagacin Aboro, Alhaji Shuaibu Suleiman Galadima, suka kuma tafi da matar da diyarsa.

Masu Kwacen Waya Sun Kai Hari Kan Malamar Jinya A Kano

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida LEADSHIP cewa bayan da aka sace su, mazauna yankin suka taru domin bin ƴan bindigar da nufin ceto su.

“Mun bi su cikin daji, amma da suka gan mu sai suka bude mana wuta. Sun kashe ɗaya daga cikinmu, Umar Abdullahi, sannan suka jikkata wani Suleiman, wanda yanzu haka yana asibiti ana kula da shi,” in ji shi.

An binne mamacin bisa tsarin Musulunci a daren ranar da abin ya faru.

Mazaunin ya roƙi gwamnati da jami’an tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto matar da diyarta, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

Advertisement

Kokarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ya ci tura, domin kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, bai amsa kira ko saƙonnin da aka aike masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Akwai yawaitar hare-haren garkuwa da mutane a wasu sassan jihar Kaduna, musamman a yankunan karkara, abin da ke kara tsananta tsoro da fargaba a tsakanin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending