Sports
IFAB Za Ta Fara Aiwatar Da Sabbin Dokokin Ƙwallon Ƙafa A Kakar 2025/26

Hukumar tsara dokokin ƙwallon ƙafa ta duniya, IFAB, ta sanar da sabbin dokoki da za su fara aiki daga kakar wasanni ta 2025/26, wadanda za su fara ne da gasar cin kofin ƙungiyoyi na duniya da za a yi a ƙasar Amurka.
Wannan mataki na IFAB ya zo da manyan sauye-sauye da suka shafi yadda ake buga wasa, da nufin inganta adalci, rage ɓata lokaci, da kuma ƙara jin daɗin masu kallon wasa.
Abubuwan Da Sabbin Dokokin Suka Ƙunsa
Gola Ya Ƙare da Daɗewa da Ƙwallo a Hannu
Daga yanzu, mai tsaron gida (gola) ba zai ƙara riƙe ƙwallo a hannunsa fiye da sakanni takwas ba. Idan ya wuce haka, za a ba wa ɗaya ƙungiyar damar yin bugun kusurwa. Wannan yana daga cikin matakan da ake ɗauka don rage ɓata lokaci a wasa.
Ƙungiya Mai Riƙe da Ƙwallo Za Ta Ci Gaba Bayan Rabin Lokaci
IFAB ta ce idan lokaci ya cika yayin da ƙungiya ke kai hari, za a ba ta damar kammala harin kafin a tafi hutun rabin lokaci. Wannan zai bai wa ‘yan wasa damar kammala yunkurinsu.
Ba a Ƙara Ba da Kati Kan Taɓa Ƙwallo da Kuskure a Gefen Fili
Idan ɗan wasa ko wani a gefen fili ya taɓa ƙwallo ba da gangan ba, ba za a ƙara ba da kati ba. Maimakon haka, za a bai wa ɗaya ƙungiyar bugun tazara kawai.
Alƙali Zai Riƙa Bayyana Hukuncinsa Ta VAR Kai Tsaye
Sabon tsarin ya ba wa alƙalin wasa damar bayyana hukuncin da ya yanke ta hanyar na’urar VAR kai tsaye ga masu kallo. Wannan zai taimaka wajen kawar da ruɗani da shakku a tsakanin ‘yan kallo.
Mai Taimaka wa Alƙali Zai Dunga Tsayawa Daidai da Gola
Don sauƙaƙa fahimtar bugun daga-kai-sai-gola, mai taimaka wa alƙali zai dunga tsayawa daidai da mai tsaron gida yayin da ake wannan bugu.
Sabon Sauyi a Bugun Daga-Kai-Sai-Gola
Idan ɗan wasa ya taɓa ƙwallo kafin bugun daga-kai-sai-gola ya cika, a yanzu zai samu damar sake bugun. A baya dai wannan kuskure na nufin rasa wannan damar, kamar yadda ya faru da Julián Álvarez a wasan Manchester City da Atlético Madrid.
Fasahar Kyamara a Jikin Alƙali
IFAB ta kuma bayyana cewa daga yanzu alƙalan wasa za su dunga sanya kyamara a jikinsu, domin ƙara haske ga yadda suke gudanar da wasa da kuma samar da ingantaccen labari ga masu kallo.
Jama’a na Sa Ran Sabon Salon Wasa
Masu sha’awar ƙwallon ƙafa a sassa daban-daban na duniya na sa ran ganin yadda waɗannan dokoki za su canza salon wasa da kuma kawo sauƙi a wajen yanke hukunci, tare da ƙara jin daɗin kallon wasa.