News
IFTILA’IN: Guguwa Mai Ƙarfi Ta Ruguza Sama da Gidaje 450 A Bauchi

Wani iftila’in guguwar iska mai ƙarfi ya afkawa unguwar Kuletu da ke cikin ƙaramar hukumar Dass a Jihar Bauchi, inda ta ruguza gidaje sama da 450, tare da barin daruruwan mazauna yankin cikin halin ƙunci da rashin matsuguni.
Lamarin ya faru ne a yammacin Lahadi, 15 ga Yuni, da misalin ƙarfe 4:47 na yamma, yayin da guguwar ta mamaye garin, tana tumɓuke rufin gidaje, tana warwatsa kaya da rushe gine-gine kamar yanda ALBARKA FM ta ruwaito.
Wani mazaunin garin mai suna Jibrin Abdullahi, wanda ke jagorantar aikin tantance asarar da aka yi, ya shaidawa wakilinmu cewa zuwa yanzu sun ƙididdige gidaje 452 da guguwar ta lalata. Ya ce ana ci gaba da gudanar da aikin domin gano yawan gidajen da abin ya shafa gaba ɗaya.
“Muna fuskantar matsanancin hali. Gidaje da dama sun rushe gaba ɗaya, wasu kuma rufin su ne kawai ya tashi. Mazauna yankin sun rasa matsuguni, sun buƙaci agajin gaggawa,” inji Jibrin.
Ya bukaci hukumomi masu ruwa da tsaki, irinsu Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA), Hukumar Kasa ta NEMA, da Gwamnatin Jihar Bauchi, da su gaggauta kawo dauki domin tallafawa al’umma da ke cikin wannan hali.
“Tunda nake a Kuletu, ban taba fuskantar irin wannan bala’i ba. Iskar ta yi ƙarfi fiye da zato. Ta rusa gidaje, ta bar mutane cikin rudani da rashin mafaka.” inji shi.
Jibrin ya kuma yi kira ga al’umma da su rika yi wa mutanen yankin addu’a, tare da nuna damuwa da jajircewa wajen tallafa musu a irin wannan lokaci na tsanani.