Connect with us

News

Majalisa Na Shirin Ƙara Yawan Alƙalan Kotun Ƙoli Zuwa 30

Published

on

Kotu
Spread the love

Majalisar Dattawan Najeriya na shirin ƙara yawan alƙalan Kotun Ƙoli daga 21 zuwa 30, domin rage cinkoson shari’o’i da ke taruwa a gaban kotun da kuma saurin yanke hukunci.

Sanata Osita Izunaso daga Imo ta Yamma ne ya gabatar da kudirin, inda ya bayyana cewa alkalai 21 ba za su iya ɗaukar nauyin yawan shari’o’in da ke taruwa a kotun ba, tun da dama daga cikinsu an nada su tun 2023.

Wata Sabuwa: Malaman Jami’ar Yusuf Maitama Sule Sun Ƙi Amincewa Da Zaɓen Sabon VC

Ya ce, “Idan alkalai 30 ne, za a iya kafa kwamitoci fiye da hudu a lokaci guda, wanda hakan zai taimaka wajen gudanar da shari’o’i cikin sauri.”

Ya kuma ce yawanci kotun koli tana yanke hukunci ne cikin rukunin alkalan da ke zama biyar ko bakwai, kamar yadda doka ta tanada.

Advertisement

Sanatan ya bayyana cewa bai kamata a bar ƙananan shari’o’i kamar rikicin haya ko rashin jituwar iyali su ɗauki dogon lokaci kafin kotu ta saurare su ba.

Ya bada misali da wata shari’a da ta shafi gadon mamata, inda ake jiran kotu tsawon shekaru uku kafin ta saurareta, duk kuwa da cewa iyalai sun warware matsalar tun da wuri.

A cikin jawabin nasa, Sanata Izunaso ya kuma ce Majalisar Dattawa na nazari kan kudirin kafa sabuwar jiha mai suna Anim a shiyyar Kudu maso Gabas.

Ya ce kudirin dokar ya riga ya tsallake karatu na biyu, kuma yanzu haka yana gaban kwamitin da ke duba sauya Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *