Connect with us

News

Dalibai 4 Cikin 10 Na Ta’ammali Da  Miyagun Ƙwayoyi – NDLEA

Published

on

IMG 20250625 WA0011 1024x7682 1

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Oyo, sun bayyana cewa matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi na ƙara kamari a tsakanin dalibai, inda kimanin dalibai huɗu zuwa biyar cikin goma ke amfani da su.

Kwamandan hukumar a jihar, Olayinka Joe-Fadile, ne ya bayyana hakan a birnin Ibadan, yayin wani gangamin wayar da kai da hukumar ta shirya a ranar Laraba, 25 ga Yuni, 2025, a matsayin wani ɓangare na shagulgulan bikin Ranar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya.

Ba Mu  Warware Rawanin Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Ba —Gwamnan Adamawa 

Taken bikin bana shi ne: “Shaida Ta Bayyana: Ku Zuba Jari a Fannin Rigakafi.”

Kwamanda Joe-Fadile ya ce binciken hukumar ya nuna cewa matsalar shaye-shaye na ƙara ƙamari a tsakanin matasa, musamman a cikin makarantu.

“Alkaluman da muke da su sun nuna cewa kimanin dalibai huɗu zuwa biyar cikin goma suna amfani da miyagun ƙwayoyi. Hakan ne ya sa hukumar ke ƙara ƙaimi wajen gudanar da shirye-shiryen wayar da kai a makarantu, daga matakin firamare har zuwa sakandare da jami’o’i,” in ji shi.

Ya ce abin takaici ne ganin cewa yanzu akwai yara ƙanana tun daga shekara tara da suka fara shan miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

A cewarsa, hukumar NDLEA ta ƙara azama wajen yakar wannan matsala, inda a cikin watannin da suka gabata, aka kama mutane 150 da ake zargi da hannu a sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Haka kuma, hukumar ta ƙone tan 11 na miyagun ƙwayoyi daban-daban da aka kama a cikin wannan lokaci.

Kwamandan ya ce domin samun nasara wajen wayar da kai, hukumar ta shiga haɗin gwiwa da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki, la’akari da irin girmamawa da jama’a ke yi musu.

“Mun fahimci cewa mutane da dama na mutunta shugabannin addini. Saboda haka mun yanke shawarar yin aiki tare da su wajen isar da saƙon mu na wayar da kai kan illolin shan miyagun ƙwayoyi,” in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mahalarta wannan gangami sun haɗa da jami’an Sojojin Najeriya, Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC), Hukumar Kwastam, Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, da kuma matasan hidimar ƙasa (NYSC), tare da sauran kungiyoyin da ke da ruwa da tsaki wajen yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending