News
Ƴan Bindiga Sun Farmaki Gidan Tsohon Minista A Filato, Sun Kashe Mace Ɗaya
Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni na Tarayya, Damishi Sango, da ke ƙauyen Dalwal a ƙaramar hukumar Riyom ta Jihar Filato, inda suka hallaka wata mata tare da jikkata jami’in ɗan sanda.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 10:46 na daren Talata, 2 ga watan Yuli, lokacin da maharan suka kutsa cikin gidan tare da buda wuta ba tare da kakkautawa ba.
Barau Ikon Allah: Siyasar Da Aka Gina A Kan Haƙuri Da Hikima
Wata majiya daga yankin ta tabbatar da cewa an harbe wata mace har lahira, wacce rahotanni ke cewa ƴar uwa ce ga tsohon ministan. Hakazalika, wani jami’in ƴan sanda mai suna Sifeta Walba Go Tom daga SPU Base 4, Makurdi, ya samu raunuka a yayin da ya yi ƙoƙarin mayar da martani.
Bayan harbin, maharan sun kwace bindigar jami’in ƴan sandan kafin su tsere ba tare da an cimma su ba.
Wasu mazauna yankin sun ce har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka iso wajen, maharan sun riga sun ɓace da gabar su.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa tuni an fara bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
