Connect with us

News

Yawan Yara Marasa Zuwa Makaranta Ya Ƙaru A Kano — Bincike

Published

on

When Kano sent almajiris home4

Wani bincike da aka gudanar a Jihar Kano ya nuna cewa adadin yara da ba sa zuwa makaranta na ƙaruwa, musamman a cikin al’ummomin karkara da masu fama da talauci.

Binciken, wanda African Institute for Solutions and Development (AISD) ta gudanar — reshen bincike na Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) — ya bayyana cewa a wasu ƙananan hukumomin Kano, kamar su Rimin Gado, Dawakin Kudu da Nassarawa, kusan kashi ɗaya cikin uku na yara ba sa halartar makaranta.

Advertisement

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da rahoton UNICEF, ya nuna cewa Jihar Kano na cikin jihohin da ke da yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya, inda adadin ya kai kusan yara miliyan ɗaya.

Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruftawar Bene Mai Hawa Uku

Shugaban tawagar da ta gudanar da binciken, Farfesa Jami’u Olumoh, ya ce yara mata su ne suka fi shan wahala, domin fiye da rabin su ba su shiga makarantar firamare.

Advertisement

Ya bayyana cewa “Yara daga yankunan karkara — kashi 86 cikin 100 — da kuma waɗanda ke cikin talauci (kashi 65%) su ne ke cikin matsala ta rashin zuwa makaranta.”

Binciken ya kuma nuna cewa wasu kabilu, musamman Kanuri da Fulani, na fuskantar ƙalubale na musamman wajen samun damar karatu.

Advertisement

Shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa Mohammad Israr, ya ce rashin ilimi barazana ce ga makomar dubban yara a Kano, yana mai cewa “Yaran da ba su zuwa makaranta su ne mafi yawan wadanda ake amfani da su a sana’o’in da suka sabawa doka, ciki har da aikatau da barace-barace.”

GWAMNATI TA YI MARTANI

Advertisement

Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano, Dakta Ismaila Danmaraya, ya ce gwamnatin jihar za ta yi amfani da sakamakon wannan bincike wajen tsara manufofi da za su rage yawan yara marasa makaranta.

Ya ce, “Zamu marawa irin wannan bincike baya, domin ya taimaka wajen ceto makomar yaranmu da kuma inganta rayuwar al’umma.”

Advertisement

A taron da aka gudanar don kaddamar da rahoton binciken a Kano, masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban sun nuna goyon baya ga binciken, tare da bayar da shawarwari kan yadda za a yi amfani da shi wajen samar da mafita ga matsalar da ta addabi fannin ilimi a jihar.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending