News
TikTok Ya Goge Fiye Da Bidiyo Miliyan 3.6 a Najeriya Saboda Saba Ka’idoji
Kamfanin kafar sada zumunta na TikTok ya sanar da cewa ya cire sama da bidiyo miliyan 3.6 daga Najeriya cikin watanni uku na farkon shekarar 2025 saboda karya dokokin da suka shafi amfani da dandalin.
Rahoton da kamfanin ya fitar mai taken Community Guidelines Enforcement Report na watannin Janairu zuwa Maris, ya bayyana cewa an dauki matakin ne a kokarin kare lafiyar masu amfani da kafar da kuma tabbatar da ingantacciyar hulɗa a tsakaninsu.
TikTok Ta Goge Fiye Da Bidiyo Miliyan 3.6 a Najeriya Saboda Saba Ka’idoji
TikTok ya bayyana cewa cikin bidiyoyin da aka goge, kashi 98.4 cikin ɗari daga cikinsu an gano su ne kafin masu amfani da dandalin su kai rahoto kansu, yayinda kuma kashi 92.1 cikin ɗari aka cire su ne cikin awanni 24 da lodasu.
A cewar rahoton, adadin bidiyon da aka cire daga Najeriya ya karu da kashi 50 cikin ɗari idan aka kwatanta da zangon baya, lamarin da ke nuna yadda kamfanin ke kara sa ido da tsananta matakan tsaro.
Sai dai TikTok ya jaddada cewa yawancin abun da masu amfani da dandalin daga Najeriya ke wallafawa yana da inganci, ilimantarwa da nishadantarwa.
Baya ga hakan, kamfanin ya dakatar da shirye-shiryen kai tsaye (LIVE) guda 42,196 tare da katse wasu 48,156 da aka gano suna ci gaba da karya ka’idojin amfani da manhajar.
TikTok ya ce zai ci gaba da aiwatar da matakai na kariya domin tabbatar da cewa dandalinsa ya kasance wuri mai aminci da amfani ga dukkan masu amfani da shi, musamman matasa.
