Connect with us

News

Jami’an Ƴan Sanda Sun Ƙwace Babura 104 A Kano

Published

on

1767915969983

Rundunar ‘yan sanda Kano ta sanar da ƙwace babura 104 da kama masu su saboda saɓa dokar da ta haramta yin “acaɓa” a cikin garin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Abdullahi Kiyawa, ya ce rundunar ta samu wannan nasara ce da taimakon sauran jami’an tsaro a Kano.

Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano

Ya ce, wannan mataki ne na tabbatar da haramcin kasuwancin zirga-zirgar mutane ta amfani da babura musamman daga ƙarfe 10 na dare zuwa ƙarfe 6 na yamma musamman ga babura masu ƙafa uku a cikin garin Kano.

A cewar Kiyawa, a cikin mako guda, jami’an tsaro sun ƙwace babura 104 da baburan “adaidata sahu” guda 68.

Waɗanda ake zargi da saɓa dokokin an gurfanar da su a gaban kotu domin hukunta su.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Bakori, ya miƙa godiyarsa ga al’umma kan haɗin kai da yaba wa haɗin guiwa da suka samu daga sauran jami’an tsaro ciki har da hukumar kula da ababen hawa ta Kano (KAROTA) wajen tabbatar da bin doka da oda.

Advertisement

‘Yan sanda sun buƙaci al’umma da su sanar da su duk wani abu da ba su yarda da shi ta lambobin waya da aka tanada: 08032419754, 08123821575, or 09029292926.

Gwamnatin Kano a watan Disamba ta jaddada dokar zirga-zirgar ababen hawa ta shekarar 2013 wacce ta haramta ɗaukar fasinjoji a kan babura a cikin garin Kano.

Dokar dai ta shafi ƙananan hukumomi 8 da ke Kano – Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa,

Tarauni, Ungogo, Dawakin Kudu (haɗi da Tamburawa, Gurjiya da Jido) da Fagge da Kumbotso.

Dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan kaso na wata 6 da tara ta Naira 10,000 da ƙwace abin hawan ga duk waɗanda suka saɓa dokar kamar yanda Jaridar premium times  ta ruwaito.

Wannan mataki na zuwa ne sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da ɓulla a Kano wadanda ke amfani da babura da ƙaddamar da hare-hare kan mazauna garuruwan da ke iyaka da jihar Katsina domin samun kuɗin fansa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending