News
Amurka Ta Bukaci Ƙananan Jami’anta Su Fice Daga Yankin Gabas Ta Tsakiya
Fadar Gwamnatin Amruka ta bukaci ma’aikatan offisoshin jakadancin ta da aikin su ba shi da wani muhimmanci su gaggauta barin ƙasashe shida na yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon damuwa da aka shiga dangane da yanayin tsaro a yankin.
Ƙasashen da matakin ya shafa sun hada da Koweït da Iraki da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahreïn sai kuma Kasar Jordan.
Wani Mutum Ya Kashe Ɗan’uwansa Bisa Tunanin A Mafarki Ne
Kazalika, ma’aikatar diflomasiyyar Amruka ta kira ƴan kasarta da su bi umurnin hukumomi tare da bibiyar ƙafofin yada labaran cikin gida don sanin da halin da ake ciki.
Tun da fari offishin jakadancin Amruka a Koweit ya sanar da kulle kofofinsa har sai yanda halin yayi saboda tsananta lamurra a yankin Gabas ta Tsakiya.
Advertisements
