Connect with us

News

Sharuɗoɗi 14 Da Ke Ƙunshe Cikin Yarjejeniyar Amurka Da Iran

Published

on

iran (1)

Amurka ta fitar da sharuɗoɗi 14 da ke ƙunshe a cikin yarjejeniyar fahimtar juna tsaƙaninta da Iran wanda ya kama hanyar kawo ƙarshen yaƙin gabas ta tsakiya da kuma buɗe mashigin ruwa na Hormuz.

Yarjejeniyar, wacce wani babban jami’in Amurka ya karanta wa manema labarai, ta fayyace wasu batutuwa har 14 filla-filla, ko da yake wasu manyan batutuwan da ba’a kai ga cimma matsaya a kansu ba, kamar batun kawo ƙarshen shirin nukiliyar Iran wanda aka bari har sai lokacin da za’a raba hannu kan yarjejeniyar ta ƙarshe, amma dai wannan ta share fagen tattaunawar kwanaki 60 da za a fara a Switzerland a gobe Juma’a.

Advertisement

Wata Gobara Ta Tashi A Gini Mai Hawa 17 A Legas

Batutuwan 14 da ke ƙunshe cikin yarjejeniyar da aka yiwa taken ” Fahimtar junar Islamabad tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran”.

Advertisement

1. Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ƙawayensu a yaƙin da aka gwabza, sun ayyana dakatar da ayyukan Soji nan take da kuma na dindindin a ɗaukacin ɓangarorin da ake gwabza yaƙi ciki har da Lebanon, kana daga yanzu babu wani da zai takali wani da faɗa ko ɗaukar wani mataki na soji a kan juna, ko amfani ƙarfi ko barazana ta kowacce hanya.

Sun kuma amince da tabbatar da mutuncin yankin da kuma ‘yancin kan ƙasar Lebanon, amma sai yarjejeniyar ƙarshe za ta tabbatar da kawo ƙarshen yaƙin har abada a dukkan fannoni.

Advertisement

Girmama ikon kowace ƙasa da ƴanci

2. Amurkar da Iran sun yi alƙawarin girmama cikekken ikon kowa, haƙƙin mallakar yankinsu, da kuma guje wa tsoma baki cikin harkokin cikin gida na juna.

Advertisement

3. Amurkan da Iran sun yi alƙawarin yin shawarwari da cimma yarjejeniyar ƙarshe cikin aƙalla kwanaki 60 da za ɗauka ana muhawara da tuntuɓar juna wadda za’a tsawaita wa’adin idan buƙatar hakan ta kama da kuma da yardar juna.

4. Da zarar an sanya hannu kan wannan yarjejeniyar, Amurka za ta fara janye ƙawanyar da ta yiwa jiragen ruwa Iran nan take, dama duk wani rikici ko cikas ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma za ta kawo ƙarshen katangar jiragen ruwa gaba ɗaya cikin kwanaki 30.

Advertisement

A wannan lokacin, zirga-zirgar jiragen ruwa za ta yi daidai da adadi ko buƙatun Iran kafin yaƙi.

Bugu da ƙari, Amurka za ta janye dakarunta a yankuna da ke kusanci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin kwanaki 30 bayan yarjejeniyar ƙarshe.

Advertisement

5. Bayan sanya hannu kan wannan yarjejeniya, Iran za ta yi shiri ta hanyar yin iya ƙoƙarinta don tabbatar da cewa jiragen ruwa na kasuwanci sun ci gaba da zirga-zirga a taku cikin kwanaki 60 ba tare da biyan haraji ko fuskantar wata tsangwama daga yankunan Tekun Fasha zuwa Tekun Oman, haka zalika Iran za ta tabbatar da cire duk wasu abubuwa masu barazana ko haɗari a cikin ruwa cikin kwanaki 30.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi tattaunawa da Sarkin Oman don fayyace makomar gudanar da ayyukan ruwa a Mashigin Hormuz, tare da tattaunawa da sauran ƙasashen gabar Tekun na Fasha bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa da kuma haƙƙin mallaka na ƙasashen bakin teku da Hormuz ya ratsa cikin su.

Advertisement

Gidauniyar sake gina Iran na dala biliyan 300

6. Amurka ta yi alƙawarin da abokan hulɗarta na yankin don samar da wani shiri mai inganci, wanda zai tara aƙalla dala biliyan 300 don sake ginawa da haɓaka tattalin arzikin Iran. Tsarin aiwatar da wannan shirin zai kammala a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar ƙarshe cikin kwanaki 60. Kuma Amurka ce za ta sauƙaka duk wasu hanyoyi da buƙata idan aka fuskanci tsaiko dangane da takunkumi.

Advertisement

7. Amurka ta yi alƙawarin kawo ƙarshen duk wani nau’in takunkumi da aka ƙaƙaba wa Iran, ciki harda waɗanda ƙudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya suka sanya mata, wato ƙudurorin Hukumar Gundarwar IAEA, da duk takunkumin Amurka, na mataki farko da na biyu, ƙarƙashin jadawalin da aka amince da shi a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar ƙarshe.

Iran da Amurka sun amince da mahimmancin batun dakatar da takunkumin da aka ambata kuma sun bayyana aniyarsu ta magance waɗannan batutuwa nan take a cikin tattaunawar don cimma yarjejeniya a kansu.

Advertisement

8. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake nanata cewa ba za ta sarrfa ko haɓaka makaman nukiliya ba, ƙasashen biyu sun amince su warware makomar uranium ɗin da tuni aka tace kuma ya ke a jibge, ƙarƙashin sa idon Hukumar Makamashi ta Duniya IAEA .

Bangarorin biyu sun kuma amince su tattauna yadda Iran za ta yi amfani da cibiyar Nukiyarta saboda bukatun farar hula, bisa ga tsarin da aka cimma a yarjejeniyar ƙarshe. Yarjejeniyar ƙarshe za ta tabbatar da tanade-tanaden wannan sakin layi.

Advertisement

Iran ta ci gaba da shirinta na nukiliya yadda yake a halin yanzu

9. Kafin yarjejeniyar ƙarshe, Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun amince Iran ta ci gaba da shirin Nukiyarta yadda ake a halin yanzu kuma Amurka ba za ta sanya sabbin takunkumi ba, ko tura ƙarin sojoji zuwa yankin.

Advertisement

10. Da zarar an sanya hannu kan wannan yarjejeniyar, Baitulmalin Amurka zai fara ɗaukar nauyin fitar da ɗanyen man Iran da sauran arbarkatun zuwa kasuwannin duniya, wajen biyan wasu ayyuka da suka shafi harkar fito ko mu’amalar banki da inshora da sufuri, da sauransu. Har zuwa lokacin da za’a cire mata takunkuman karya tattalin arziki.

11. Amurka ta yi alƙawarin samar da cikakkiyar dama ga Iran ta yi amfani da kuɗaɗen da aka daskarar bayan aiwatar da wannan yarjejeniyar, Amurka da Iran za su amince da juna kan hanyoyin da suka shafi sakin waɗannan kuɗaɗen yayin tattaunawar.

Advertisement

12. Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun amince cewa za a kafa wata hanyar zartaswa don sa ido kan nasarar aiwatar da wannan yarjejeniyar da kuma bin diddigi na share fagen yarjejeniyar ƙarshe.

13. Da zarar an sanya hannu kan wannan yarjejeniyar, da fara aiwatar da buƙata da aka ambata a lambobi na 1 da 4 da 5 da 10 da kuma 11 na wannan yarjejeniyar, kai tsaye za’a ci gaba da fara tattaunawa kan yarjejeniyar ƙarshe.

Advertisement

14. Yarjejeniyar ƙarshe za ta sami amincewar zaman Majalisar Ɗinkin Duniya ta yadda kai tsaye ƙudirin ya koma doka.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending