News
NSCDC Ta Gano Jami’ar Bogi Da Ke Karɓar Har Naira Miliyan 1.5 A Legas
Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta ce ta bankado wata jami’ar bogi da ake gudanar da ita a cikin wani gida mai dakuna uku a yankin Ilado, da ke ƙaramar hukumar Olorunda LCDA a Jihar Legas.
Hukumar ta bayyana cewa ta ceto matasa 106 da ake zargin an yaudare su da alkawarin ba su gurbin karatu, bayan da jami’anta suka kai samame a cibiyar a safiyar Litinin.
CBN: Umarnin Akanta Janar Ya Sa Muka Buɗe Wa PFIPC Asusu
A cewar NSCDC, binciken sirri da ta shafe kwanaki tana gudanarwa ne ya kai ga gano cibiyar, tare da kama mutumin da ake zargin shi ne ke jagorantar ayyukanta.
Binciken farko ya nuna cewa cibiyar ba ta da rajista ko amincewar hukumomin da ke kula da manyan makarantu a Najeriya. Duk da haka, tana tallata kanta ta kafafen intanet a matsayin cibiyar koyon karatu ta nesa mai alaƙa da wata jami’a a ƙasashen waje.
Hukumar ta ce mafi yawan waɗanda aka ceto masu shekaru ne tsakanin 19 zuwa 24, kuma sun fito daga jihohi daban-daban na Najeriya, da kuma ƙasashen Nijar, Kamaru da Togo.
Rahoton binciken ya kuma nuna cewa waɗanda abin ya shafa sun biya kuɗaɗen rajista da gudanarwa da suka kai tsakanin Naira 200,000 zuwa Naira miliyan 1.5, yayin da wasu daga cikin ‘yan ƙasashen waje suka biya tsakanin dala 400 zuwa 500.
NSCDC ta ƙara da cewa bincikenta ya gano ana kuma tilasta wa mahalarta shirin su nemo sababbin ɗalibai domin samun kuɗi, tsarin da hukumar ta ce yana da alamun kamanceceniya da damfarar Ponzi.
Kwamandan NSCDC na yankin Badagry, CSP Gbenga Ekunola, ya ce za a ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke da hannu a lamarin, tare da tantance ko akwai irin wannan cibiyoyi a wasu sassan ƙasar.
Ya ce za a gurfanar da duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa a gaban kotu, yayin da za a mayar da waɗanda aka ceto ga iyalansu bayan kammala bincike.
