Business
Matatar Dangote Za Ta Buɗe Sayar Da Hannayen-Jari Na Naira Tiriliyan 2.15
Matatar man Dangote za ta buɗe sayar da hannayen-jarinta na farko ga jama’a (IPO) ranar Litinin, lamarin da zai bai wa masu zuba jari damar mallakar wani kaso a matatar mai mafi girma a Afirka.
Za a ƙaddamar da hannayen-jarin a yau Litinin 14 ga Satumban 2026, a hukumance a wani biki da za a gudanar a zauren hannun-jari na Kasuwar Hannun-Jari ta Nijeriya (NGX) da ke jihar Legas.
Jirgin shahararren mawaki Ya Kauce Hanya, Ya Kama da Wuta A Brazil
Matakin zai bai wa jama’a damar mallakar hannun-jari a babban matatar mai na Afirka wanda kuma ke zama ɗaya daga cikin manyan masana’antu masu matuƙar muhimmanci a duniya, hannun-jarin, ya ƙunshi sabbin hannayen-jari biliyan 4.1, inda za a sayar da kowanne kan Naira 525.
Mafi ƙanƙantar adadin da mutum zai iya saya shi ne hannun-jari 10, wanda ya kai Naira 5,250. Kana ana sa ran za a rufe tayin sayar da hannayen-jarin a ranar 13 ga watan Oktoba, bisa sharuɗɗan da ke cikin takardar bayanin tayin.
Kazalika ana sa ran hannayen jarin matatar (IPO) zai tara kusan Naira tiriliyan 2.15, adadin da ake ganin zai kasance cikin manyan hannayen jari da aka taɓa sayarwa a Afirka.
Kamfanin Dangote ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen faɗaɗa ayyukan matatar, tare da gudanar da wasu manyan tsare-tsare da kuma zuba jari a ayyukan da za su taimaka wajen bunƙasa kamfanin.
Shugaban rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa sayar da hannayen jarin wani mataki ne na bai wa ’yan Nijeriya da ’yan Afirka da sauran masu zuba jari dama a ci gaba da kuma bunƙasar matatar.
