Connect with us

News

Cikin Watanni Shida Mun Kawo Karshen Matsalar Tsaro -Shattima

Published

on

Advertisements
ads

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

Mataimakin Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya ce idan aka zabe su a 2023, gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu za ta kawo karshen tada kayar baya cikin watanni shida zuwa shekara guda.

Advertisement

 

Ya bayyana haka ne a yayin wani taro da aka yi tsakanin Tinubu da ‘yan kasuwa a Legas.

Buhari Ya Kuduri Aniyar Gudanar Da Sahihin Zabe A Najeriya  – Fadar Shugaban Kasa

“A cikin watanni shida da shekara daya, shugabana (Tinubu) zai hada kai shugabannin tsaro don kawo karshen wannan hauka,” in ji shi.

 

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da aka bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mutum mai iya mayar da bola zuwa dukiya.

Advertisement

 

Darakta-Janar na Kwamitin yakin neman zaben Shugaban kasa na APC kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ne ya bayyana hakan a taron da ake yi na tattaunawa tsakanin Tinubu da ’yan kasuwa masu zaman kansu masu zaman kansu a Legas.

 

Lalong ya ce Tinubu shi ne ya fi kowa a cikin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 domin yana da tarihi na mayar da abun da ya lalace zuwa arziki.

 

“A gare mu a APC tallata Tinubu/Shettima ga ‘yan kasuwa ba abu ne mai wahala ba domin Asiwaju hamshakin dan kasuwa ne wanda ya abubuwan cigaba.

Advertisement

 

“Tinubu na da sha’awar kawo ci gaba ga dukkan ‘yan Najeriya,” in ji shi.

 

Ya bukaci ‘yan kasuwa da su marawa Tinubu baya domin yana da sha’awar hada kai da su wajen samar da ayyukan yi da gina tattalin arziki mai inganci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending