Connect with us

News

El-Rufa’i Ya Shawarci Gwamnatin Tarayya Da Ta Gaggauta Cire Tallafin Man Fetur.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta cire tallafin man fetur.

 

Advertisement

Ya yi wannan kiran ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ke gudana a Abuja.

Kotu : tuhumar mutane 26 bisa laifin satar danyen Mai

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, a lokacin da a ka tambayi gwamnan, wanda ke jawabi a zagayen tattauna wa a taron, kan ko me ya kamata gwamnati ta sa gaba, sai ya ce, “a cire tallafin man fetur nan take.

Advertisement

 

El-Rufai ya bayyana cewa gwamnonin jihohi 36 da jami’an gwamnatin tarayya, a majalisar tattalin arzikin kasa, sun amince da cire tallafin man fetur a watan Satumban 2021.

Advertisement

 

Ya bayyana mamakin sa da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa aiwatar da wannan kuduri, duk da tsananin matsin tattalin arziki da tallafin ya janyo wa kudaden gwamnati da kuma almundahana da ke tattare da hakan.

Advertisement

 

A cewarsa, gaskiyar yadda ake tafiyar da tallafin, wanda ya kamata a ce gwamnatin tarayya ta kawo karshen sa tun kafin yanzu ya kasance cikin shakku.

Advertisement

 

Gwamnan ya kuma ce, Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa, NEC, ta yi hasashen cewa, idan ba a cire tallafin ba, lokaci zai zo da kamfanin man fetur na ƙasa, NPL, zai ce an kashe daukacin kudaden da kasar ke samu a duk wata wajen bayar da tallafi.

Advertisement

 

Ya ce: “Masu tsara kundin tsarin mulkin mu sun yi hasashen cewa domin tattalin arzikin ya yi aiki yadda ya kamata, ya kamata a samu daidaito tsakanin gwamnatocin tarayya da na jihohi.

Advertisement

 

“Don haka ne aka kafa Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa, inda Mataimakin Shugaban Kasa ya zama Shugaba. Dukkanin gwamnoni 36 mambobi ne da wasu jami’an gwamnatin tarayya kamar ministan kudi.

Advertisement

 

“A karkashin wannan gwamnatin, kusan duk wata muna haduwa a addini, domin tattalin arzikinmu daya ne kawai,” in ji shi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending