News
An rantsar da Anwar Ibrahim a matsayin sabon Firaiministan Malaysia
DAGA. KABIRU BASIRU FULATAN
An rantsar da Anwar Ibrahim a matsayin sabon Firaministan Malaysia lamarin da ya kawo ƙarshen rikicin siyasar da ya biyo bayan zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.
Sarki Sultan Abdullah ne ya naɗa shi bayan shafe ƴan kwanaki yana tuntuɓa domin kafa gwamnatin haɗaka.
Kotu ta soke takarar dan Landon da ya tsaya takara a jam,iyyar APC
Wani mai goyon bayan Mista Anwar yake cewa na yi farinciki matuƙa da wannan labarin. Mun daɗe muna jiran rana irin haka kuma lokaci ya yi da za mu yi maraba da wanda zai kawo wa Malaysia kyakkyawan sakamako.
Mista Anwar dai ya shafe shekaru ashirin da biyar yana neman kujerar Firaminista a Malaysia.
A tsukin lokacin kuma ya sha ɗauri sau biyu na tsawon shekara tara bayan samunsa da laifin aikata lalata– tuhumar da ya sha musantawa tare da cewa an yi ne domin a ɓata masa suna.
