News
Ana cin zarafin yara fiye da kowa a Kano – NHRC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ofishin Hukumar kare haƙƙin bil’adama ta Najeriya a jihar Kano ya ce ya samu rahoton cin zarafi mai nasaba da jinsi guda 1,300 daga watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2022.
Kuma a cewar shugaban ofishin, Shehu Abdullahi, ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara tara ne suka fi fuskantar cin zarafin, haka nan lamarin ya kai ga mutuwar wasu daga cikin su da kuma haifar da lalurar ƙwaƙwalwa.
Duk Makarantar da aka kama suna magudin jarrabawa za, a dakatar da ita na shekaru biyu, in ji NECO
Abdullahi ya bayyana haka ne a wani taron da aka gudanar domin tunawa da ranar masu fafutika ta duniya, ta shekarar 2022.
Jami’in ya ce ya zama wajibi a haɗa hannu tsakanin masu ruwa da tsaki domin kawar da matsalar.
Advertisements
