Opinion
Yakamata Shugaban NANS ya tashi tsaye wajen nemawa Dalibai makomar su ta gobe tun kafin a kada kuriar zaben 2023.
Yakamata Shugaban kungiyar Dalibai ta kasa NANSS ya tashi tsaye wajen nemawa Dalibai makomar su ta gobe tun kafin a kada kuriar babban zabe 2023 mai zuwa a wajen yan takarkarun kujerar shugaban kasa
Duba da yadda ake kokarin karin kudin makarantun Jami a wanda hakan babban matsala ce ga rayuwar alummar ta gobe.
musammam idan akayi guba ga yaya talakawa saboda a yanzu ma wasu da dama daga cikin dalibai iyayen su ba su da karfin da za su iya biyawa ya’yan su kudin makarantar.
Hakan yasa Dalibai su ke shiga kafafan yada labarai domin neman temako a gurin alummar dan neman kudin da ake biya mutane su nayi fafutuka su ga sun yi iyabakin kokarin su domin ganin sun samu sun yi karatun to ina ga Kuma anninninka kudin makarantar idan kuma ba so akeyi a ga abun yagagari mutane ba wanda kuma bama fatan hakan.
Binciken da nayi yanuna cewa hakan babban matsala ce ga alummar kasa baki daya saboda hakan zai iya haifar mana da munanan abubuwa masu yawa.
Saboda haka ku shuwagabannin Dalibai na kasa hakki ne akan ku da kufuto ku jarjirce wajen nemawa Daliban gobe masu zuwa sauki domin samarwa da kasar ku gobe mai kyau, ku futo ku zauna da kowane takarar shugaban kasa kuji idan Allah ya ba shi Mulki menene makomar Dalibai a dangane da karin kudin makarantar Jami a da ake shirin yi musammam ma manyan jam,iyun da su kafi magoya baya, sannan kuma bayan kun tattauna da su ku futo kafafan yada labarai ku yi wa jama a bayanin yadda kukai da kowa kuma duk wanda kuka zauna da shi komai za ku yi ku yi a rubuce kuma ku sa lauya ku ne temako daga kungiyar lauyoyi ta kasa.
Comr Abba Alra-iwas
