Politics
Nafi kowanne Dan Takarar Majalisar Tarayyar A Nasarawa Chanchanta— Kaka
Dan takarar majalisar tarayyar Mai wakiltar karamar hukumar nasarawa a karkashin inuwar jam iyyar PRP ahmad Muhammad Saleh kaka yace yafi kowanne Dan takarar nassarawa chanchanta da wannna kujerar.
Kaka ya bayyana hakanne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Jaridar indaranka a jiya alhamis
Yace Al,ummar nasarawa suna bukatar mutum Mai ilimin addini dana zamani Wanda yasan matsalolinsu na yau da kullum kuma matashi kuma dan gwagwarmaya kamar sa.
Dan takarar majalissar yace zai magance matsalolin da karamar hukumar nasarawa kefuskan ta hanyar gabatar da kudiri a gaban majalisar
Yace idan har Jama,ar karamar hukumar nasarawa suka zabeshi tom zasu Fi kowace Al umma Jin Dadi a bangaran wakilci tarayya
Advertisements
