Sports
Kylian Mbappe ya kafa sabon tarihi a PSG
Kylian Mbappe ya kasance dan wasan da ya fi ci wa Paris St-Germain kwallo a Gasar Ligue 1 bayan sun doke Lens da ci 3-1 ranar Asabar.
Hakan ya sa sun zama na daya a saman tebirin gasar da maki biyar.
Mbappe, wanda ya zura jimillar kwallo 139 a wasan lig 169 da ya yi wa kulob din, yanzu ya zarta adadin kwallon da Edinson Cavani ya ci.
Mbappe da Lionel Messi da kuma Vitinha ne suka ci wa PSG kwallo, yayin da Przemyslaw Frankowski ya ci wa Lens tata kwallon ta hanyar bugun fenareti.
Messi da Mbappe sun ci wa PSG kwallo 23 a wannan shekarar, kuma watakila wannan shi ne abu mafi muhimanci da ya faru a kulob din a bana.
Ko da yake wannan bajinta ba za ta warware matsalolin da PSG ke ciki ba, amma za ta taimaka musu wurin daukar Kofin Lig karo na 11.
Trt world Africa
-
News5 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News7 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
