Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Daba Da Ke Amfani Da Wuƙaƙe Don Cutar Da Mutane A Kano.

Published

on

Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Daba Da Ke Amfani Da Wuƙaƙe Don Cutar Da Mutane A Kano.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tace  ta kama wasu da ake zargi da aikata daba ta hanyar amfani da wuƙaƙe suna gallaza wa mutane a birnin Kano.

 

A cewar bayanai daga wajen waɗanda ayyukan ƴan dabar ya shafa, sun ce mutanen da ake tuhuma kan yi amfani da tituna masu cunkoso da wuraren taron jama’a don aikata ta’asar.

 

Advertisement

Duk da matsalar rashin tsaro, ta kasance cikin kwanciyar hankali har sai da aka samu gungun masu riƙe da wuƙaƙe.

 

Ayyukan ƴan dabar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bayan far musu da ɓata garin suka yi, yayin da waɗanda suka samu tsira kuma ke gamuwa da munanan raunuka.

 

’Yan dabar – waɗanda rundunar ‘yan sandan ta Anti-Daba ta kama – sun yi ƙaurin suna wajen amfani da wurare masu cunkoso don cin zarafin jama’a da rana tsaka.

 

Advertisement

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi kira ga jama’a da su taimaka rundunar wajen gano sauran ‘yan ƙungiyar dake cikin ƙwaryar birnin Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending