Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur

Published

on

 

Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur daga watan Yunin wannan shekara.
Ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Ahmed Zaniab ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, jim kadan bayan taron majalisar tattalin arzikin kasa,wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Advertisement

 

Munafunci ne musababin  masu tada zaune tsaye a yakin Sudan–Aminu khan

Ta ce anyi nazari sosai kan lamarin inda ta kai ga yanke shawarar cewa ba zai dace a cire tallafin ba da zarar sabuwar gwamnati ta yi kokarin sasantawa kan harkokin mulki.

Advertisement

Ta kuma bayyana cewa akwai bukatar a kara fadada kwamitin da ake da shi wanda ke tattaunawa kan batun tallafin man fetur domin samar da karin bayanai daga ‘yan Najeriya da abin ya shafa.

Ta kuma ce akwai bukatar a kara yin mu’amala da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kara cudanya da kungiyar dillalan man fetur da dai sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending