News
JAMB Ta Sanya Ranar Fitar da Sakamakon Jarabawar UTME 2023

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta JAMB a ranar litinin ta ce za ta fara fitar da sakamakon jarabawar UTME a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023.
Hakan na kunshe ne a karshen wani taron gaggawa da aka gudanar a karshen mako a Abuja.
A cikin ‘yan mintoci da sakin sanarawa wadda aka bai wa wakilinmu a safiyar ranar Litinin, hukumar ta lura da cewa an samu tsaikon fitar da sakamakon ne saboda tana son ganin an kammala duk wani binciken da ya dace.
“Hukumar za ta fitar da sakamakon ‘yan takarar, wadanda suka yi jarabawar zuwa yanzu a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023.
“Hukumar ta jinkirta fitar da sakamakon ne don tabbatar da cewa an kammala dukkan binciken da ya dace baya ga tabbatar da cewa ma’ana da karkatar da su sun yi daidai kafin
fitar da wadannan sakamakon.
“Yayin da ‘yan takara zasu iya tantance sakamakonsu a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023, wadanda suka zana jarrabawar amma suka fuskanci kalubale ba tare da sanin haka ba, ba za su ga sakamakonsu ba, sai dai su ga sanarwarsu don sake zana jarabawar,” inji ta.
