Connect with us

News

Daya Daga Cikin Motocin Da Ke Kwaso ‘Yan Najeriya a Sudan Ta Kama Da Wuta

Published

on

Ɗaya daga cikin motocin da ke kwaso ƴan Najeriya daga Khartoum babban birnin ƙasar Sudan, zuwa tashar jirgin ruwan Sudan, inda daga nan za su shiga Saudiyya, ta kama da wuta.

A cewar rahoton Legit.ng, lamarin ya auku ne ranar Litinin 1 ga watan Mayu, jim kaɗan bayan motoci 26 da suke ɗauke da ƴan Najeriyan sun bar Al-Razi da misalin ƙarfe 12 na dare domin zuwa tashar jirgin ruwan Sudan.

Advertisement

An kashe mutane fiye da 500 a Kudancin Kaduna cikin shekara 6

Wutar da ta kama a motar wacce ke ɗauke da ɗalibai 50 da aka yi wa laƙabi da (Katsina 1), ta auku ne a dalilin zafin da ɗaga daga cikin tayoyin motocin ta yi.

Sani Aliyu, wanda ya ke a Sudan, ya bayyana cewa:

Advertisement

“Dr Hashim Idris Na’Allah, shugaban ƙingiyar dattawan Najeriya na Sudan, yana daga cikin fasinjojin da ke cikin motar, wacce ke dauke da ɗalibai 50 (maza 49 da mace 1).”

Aliyu ya ƙara bayyana cewa, lamarin ya auku da misalin ƙarfe 2:30 na dare a agogon Sudan, jim kaɗan bayan direban ya tsaya a wajen bincike na RSF, inda a nna tayar ta yi bindiga wacce ta sanya wutar ta kama.

Advertisement

Ya ce babu wani daga cikin fasinjojin da ya jikkata domin sun samu sun fice daga motar.

An sanya fasinjoji 40 zuwa sauran motocin, yayin da ragowar mutum 10 suka kwana a wajen bincikeɓ RSF ɗin tare da direbobin.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending