Connect with us

News

Wasu Yan bindiga sun sace manoma a jihar Neja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da manoma a wani ƙauye da ke karamar hukumar Paikoro.

Wasu daga cikin mazaunan ƙauyen na Kaffin-Koro sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shafe tsawon sa’o’i suna cin karensu babu babbaka, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa.

yaki da talauci  na  daya daga cikin manyan abubuwan da ya sa a gaba—-Umar Namadi

An kai hari ne a ranar Labara a yankuna da dama da ke ƙauyen, sannan akwai mutum ɗaya da aka kashe.

Babu dai wasu cikakkun bayanai kan adadin manoman da aka yi garkuwa da su, sai dai yankin Neja na daga cikin yankunan Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga domin neman kudin fansa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending