Connect with us

News

An Cafke Kananan Yara 5 Kan Ayyukan Matsafa A Kwara

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Yan sanda sun tsare wasu kananan yara maza uku da mata biyu kan zargin ayyukan kungiyar matsafa da kuma sace-sace a Jihar Kwara.

Kakakin ’yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi, ya ce, “An kwace makamai da miyagun kwayoyi da kuma ganye da ake zargin tabar wiwi ce a hannun kananan yaran.”

Advertisement

Ya ce dubun kananan yaran ta cika ne a ranar 26 ga watan Afrilu a wata matattarar bata-gari da ke yankin Gambari/Oja Gboro.

An Kama Dan Shekara 23 Da Kunshi 605 Na Tabar Wiwi A Jahar Kano

Ya ce, “Bayan samun bayananan sirri jami’anmu suka kai samame a dabar da ke kusa da Kokewu-Kobere a unguwar Oja Gboro, inda su aka kama su biyar din.”

Advertisement

Ya ce an gano yaran mambobin wata kungiyar asiri ce da ke addabar jama’a suna kwace musu kayayyaki a yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending