Connect with us

News

Gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da rushe gine ginen da aka yi a wurare mallakar Gwamnatin.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da aikin rushe rushen gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a filayen gwamnati da ke fadin jihar Kano.
A wannan rana an rushe gine gine-ginen da aka yi a cikin Daula Hotel da kuma sansanin alhazai a cikin daren jiya.
Da safiyar ranar Asabar ne aka fara rusa wasu gine-gine a filin sukuwa domin ƙwato filin gwamnati kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin ta fitar a ranar Asabar ta bayyana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin rushe dukkan haramtattu gine-gine akan filayen gwamnati a cikin makarantu, asibitoci, masallatai, makabartu, kasuwanni, da sauran su.
Idan za a iya tunawa a alƙawuran yaƙin neman zaɓe da gwamnan ya yi, ya alƙawarta ƙwato filaye mallakar gwamnati da aka gina ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnatin ta yi kira ga mazauna Kano da su yi haƙuri, kasancewar sabuwar gwamnatin na son tabbatar da ci gaban jihar.
Dama dai a jawabin da sabon gwamna ya yi bayan shan ranstuwar kama aiki ranar Litinin, ya bayar da umarni ga jami’an tsaro da su ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da ya ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sayar wa wasu mutane a jihar.
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending