News
Ma’aikatan Lafiya Sun Janye Yajin Aiki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ma’aikatan lafiya na Najeriya sun janye yajin aikinsu na kwana 12 bayan wata ganawa da suka yi da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu a jiya Litinin.
Ƙungiyar ma’aikatan ta JOHESU, wadda ta yi ganawar da shugaba Tinubu, ta ce ta yanke shawarar janye yajin aikin ne domin bai wa gwamnati wa’adin mako uku domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.
Mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dr Obinna Ogbonna ya ce “an samu ci gaba” a tattaunawar da suka yi da shugaban ƙasa.
“Amincewa tamkar abu ne mai haɗari, amma tunda a yanzu muna magana ne da sabon shugaban ƙasa, wanda da kansa ya roƙi mu ba shi lokaci, ya kamata mu ba shi.
“Bayan kwanakin 21 za mu duba inda ake sannan mu ɗauki mataki na gaba.” in ji Dr Obinna
Ma’aikatan lafiyar dai na nema ne a yi watsi da tsarin biyan albashi na bai-ɗaya, da biyansu alawus-alawus ɗin aiki, da sake duba shekarun yin ritaya da dai sauran su.
