News
SUDAN:Makaman roka sun kashe ‘farar- hula 16’ a Sudan
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Akalla farar-hula 16 ne suka rasu bayan makaman roka sun fada kan gidajensu a yammacin Darfur na Sudan, kamar yadda wata kungiya ta lauyoyin yankin ta bayyana a ranar Asabar.
Yankin mai girma, wanda tuni yaki ya daidaita a farkon shekarun 2000, ya fuskanci rikice-rikice mafi muni tun a tsakiyar watan Afrilu a tsakanin janarorin Sudan biyu masu adawa da juna.
Bakuwar Tsutsa Ta Kori Mazauna Unguwar Gayawa Gandu Daga Gidajensu A Kano
“A lokacin musayar wuta ta hanyar makamin roka tsakanin sojojin kasar da kuma dakarun RSF, farar-hula 16 suka rasa ransu a ranar Juma’a, kamar yadda wata kididdiga ta wucin-gadi a Nyala ta bayyana,” in ji kungiyar.
Haka kuma maharbin boye ya kashe akalla mutum daya, kamar yadda kungiyar ta kara da cewa.
A El Geneina babban birnin Yammaci Darfur, a kusa da Chadi, rahotanni sun ce maharban boye sun ta kokarin harbin mazauna gida daga saman kwanon gidaje tun bayan da aka soma yakin, haka kuma dubban mutane sun tsere inda suka tsallaka iyaka.
Yakin, wanda ya barke a babban birnin Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu sa’annan ya bazu zuwa Darfur duk a cikin watan, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3,000 a fadin Sudan, kamar yadda aka kiyasta.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
