Connect with us

News

SAMAR DA TSARO: Gwamnatin Kaduna za ta dauki matasa ‘yan sa kai 7,000

Published

on

Gwamnan Jahar Kaduna Uba Sani
Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani a ranar Litini ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta dauki matasa 7,000 a horas da su don kara kaimi wajen fatattakar batagari a fadin jihar.

Gwamna Sani ya ce matasan da za a dauka a kuma horas da su za su yi aiki ne a karkashin kungiyar ‘yan bangan Jihar wanda gwamnati ta san da zaman su.

An Dawo Da Shirin Bautar Kasa A Borno Bayan Shekara 13

Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin inganta tsaro a fadin jihar.

“Zuwa yanzu muna da ‘yan bangan akalla mutum 2,000. Idan muka dauki karin mutum 7,000 za su kai 9,000 kenan.

“Gwamnati za ta horas da matasan tare da hadin guiwar ‘yan sandan jihar, sannan kuma da rundunar DSS da kuma sanin Sojoji. Bayan haka za horas da su ne a kwalejin ‘yan sanda dake Kaduna.

Advertisement

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta hada kai da masu unguwanni da shugabannin addinai domin kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending