Connect with us

News

Ambaliyar ruwa ta raba akalla mutane 563 da muhallansu a a jahar Adamawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ambaliyar ruwan sama ta raba mutane 563 da ke Unguwan Tana a Ƙaramar Hukumar Yola ta Gabas a jihar Adamawa da muhallansu.

Mutanen da iftila’in ya shafa, a yanzu haka sun samu mafaka a makarantar sakandare ta je ka ka dawo ta GDS da ke yankin Limawa-Jimeta, a Yola babban birnin jihar.

Sakataren Gwamnatin Gombe Ya Rasu Ana Saura Sati Daya Yayi Ritaya

Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa, mutanen da abin ya shafa sun tare a ajujuwa bakwai na makarantar.

Kazalika, mataimakin gwamnan jihar Kaletapwa George Farauta, ya ziyarci Unguwan Tana domin duba irin varnar da ambaliyar ruwan ta janyo.

Bugu da ƙari, George ya yi alƙawari gwamnatin jihar, za ta kawo masu ɗauki domin a rage masu raɗaɗin zafin aukuwar iftila’in na ambaliyar ruwan.

Advertisement

Amabilayar ruwan dai ta auku ne sanadiyyar cikar da kogin Benuwe ya yi biyo bayan yin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da kuma sako ruwan Dam na Lagdo da ke a jamhuriyar Kamaru.

A wani labarin kuma Sakataren Gwamnatin Gombe Ya Rasu Ana Saura Sati Daya Yayi Ritaya

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending